Thursday, 6 June 2019

Gwamnan Kano da wakilanshi sun halarci hawan Sallah a sabbin masarautun jihar amma babu wakilin gwamnati a hawan masarautar Kano

Wadannan hotunan hawan Sallah ne da aka yi a garin Bichi na jihar Kano inda me martaba sarkin Bichin, Aminu Ado Bayero ya jagoranta wanda ya samu halartar Gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.Manyan jami'an gwamnatin jihar da suka hada da mataimakin gwamnan, Sakataren gwamnati, shugaban majalisar jihar duk sun halarci hawan sallar da aka yi a wasu daga cikin sabbin masarautun da gwamnatin jihar ta kirkiro irin su, Karaye, Rano da Gaya.

Wata sanarwa da sakataren watsa labaran na gwamna ya fitar ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa hawan da aka yi a masarautar Bichi.

Shi kuwa mataimakin gwamnan na Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci wata tawagar zuwa hawan da aka yi a masarautar Rano, yayin da shugaban majalisar dokokin jihar Kanon, Kabir Alhasan Rurum ya jagoranci tawagar jami'an gwamnati zuwa hawan da aka gudanar da masarautar Karaye.

Shi kuwa sakataren gwamatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya jagoranci wata tawagar zuwa masarautar Gaya.

Sai dai babu wani wakilin gwamnati da ya halarci hawan Daushe da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya gabatar a ranar Laraba.

No comments:

Post a Comment