Friday, 7 June 2019

Gwamnati ta rufe AIT da Raypower

Hukumar da ke kula da gidajen Talabijin da Rediyo ta Najeriya, NBC, ta dakatar da lasisin kafar watsa labarai ta DAAR Communications, mai gidan talabijin na AIT da gidan rediyo na Raypower a Najeriya na wucin gadi.


Hukumar ta ce kafar watsa labaran ta karya dokarta mai tsauri da ta hana watsa abubuwan da za su iya haddasa gaba da rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan kasa.

Hukuncin dai ya shafi dukkan tashoshin kafar watsa labaran da ke Najeriya da suka hada da gidan talabijin din AIT da gidan rediyo na Raypower.


Sakataren hukumar ta NBC, Muhammad Mujtaba Sada, ya bayyana wa BBC cewa hukumar ta sha bai wa kafar watsa labaran shawarwari kan yadda take gudanar da ayyukanta wadanda suka saba wa kundin tsarin watsa labarai na kasa.

"Wannan kundin dokoki ba NBC ce kawai ta zauna ta yi shi ba, da su kafofin watsa labaran aka zauna aka yi kuma suka rattaba hannu, suka amince", a cewarsa.

Ya ce kuma duk wata kafar watsa labarai da za a bai wa lasisi, sai ta sa hannu kan cewa ba za ta yada wasu shirye-shirye masu dauke da kalaman nuna batanci ga addini ko harshe ba, ko kuma wani abu da zai nemi wargaza kasar ba.

Sai dai hukumar ta ce kamfanin DAAR din ya yi watsi da wannan doka, abin da ya ja masa dakatarwar ta wucin gadi.

"Dama can ana gayyatarsu su akai-akai, sannan an zauna da su kuma an gaya masu abin da suke yi ba dai-dai ba ne," in ji Muhammad Mujtaba Sada.

Ya ce a yanzu abin ya kai makura shi ya sa har aka dauki wannan mataki.

Sai dai ya ce yanzu dole ne a zauna a sasanta tsakanin hukumar NBC da kamfanin na DAAR tun da duk hanyoyin da aka bi a baya ba su yi aiki ba.

A martaninsa shugaban kamfanin na DAAR, Raymond Dokpesi Junior, a wata sanarwa ya ce, ya zama dole su rufe tashoshinsu domin bin umarnin dakatarwar da NBC ta yi musu.

Amma kuma ya ce za su bi mataki na shari'a domin ganin an kawar da wannan hukunci na dakatarwar don tashoshinsu na talabijin na AIT da na rediyon Ray Power sun koma aiki.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment