Saturday, 8 June 2019

Gwamnatin Kano ta haramta taron gangamin jama'a


Rundunar 'yan sandan Kano ta haramta duk wani taro na gangamin jama'a a fadin jihar.


Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna ya fitar ta ce an haramta zanga-zanga da duk wani taro da ya shafi gangamin jama'a a fadin jihar har sai baba ta gani.

Wannan matakin na zuwa ne bayan da rashin jituwa tsakanin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ta kara fitowa fili bayan da gwamnan ya aike wa da Sarki takardar neman bahasi kan tuhumar da ake yi wa sarkin na yin bushasha da makudan kudaden masarauta.A cikin sanarwar, rundunar 'yan sandan jihar ta ce an dauki matakin ne don kaucewa duk wata barazana ga zaman lafiya da kuma karya doka baya ga matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Sanarwar ta yi gargadi ga jama'ar kasar da kungiyoyin farar hula su mutunta dokar wacce a sanarwar ba a fadi lokacin dage ta ba.


Sanarwar ta ce duk wanda aka kama da laifin saba dokar da za kama shi kuma a hukunta.

Gwamnatin jihar Kano dai ta ba Sarki Sanusi awa 48 da ya bayar da bahasin yadda ya kashe kudaden masarautar da ake zargin an kashe ba bisa ka'ida ba.

A ranar Litinin ne dai hukumar karbar korafe-korafen jama'a ta jihar, ta nuna cewa Sarki Sanusi ya yi bushasha da kudin masarauta inda kuma ta nemi da a dakatar da sarkin.

Tun bayan da gwamnan Kano abdullahi Umar Ganguje ya kirkiro sabbin masarautu ake ganin akwai babban sabani tsakanin shi da Sarki Sanusi.

Sai dai gwamnatin Kano ta dade tana cewa babu wani sabani tsakaninta da masarautar Kanon, kuma ta kirkiri masarautun ne domin samar da ci-gaba, to sai dai abubuwan da suke faruwa a zahiri sun nuna sabanin hakan.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment