Sunday, 9 June 2019

Har yanzu ba'a yi sulhu ba tsakanin Gwamna da sarkin Kano ba

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ba'a sasanta gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da sarkin Kanon, Muhammad Sanusi na II ba kan rashin jituwar dake tsakaninsu ba.Rahoton Daily Trust yace wani na hannun damar gwamnan ya bayyanawa jaridar cewa tabbas an yi zaman sulhun wanda kuma gwamnan da Sarkin duk sun halarta a Abuja. Amma har yanzu ba'a cimma matsaya ba dan gwamnan bai fayyace shawarar da ya yanke ba akan lamarin.

No comments:

Post a Comment