Sunday, 9 June 2019

Hazard ya shiga jerin 'yan kwallo 10 da suka fi tsada a Duniya


Kudin da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sa yi dan kwallon Chelsea, Eden Hazard, watau sama da Yuro 100 sun sa dan wasan ya shiga sahun 'yan kwallo 10 da suka fi tsada a tarihi.Madrid din ce dai ta kasance kungiyar da ta sayi dan wasa  mafi tsada a Duniya a shekarar 2013 lokacin da ta sayo Gareth Bale daga Tottenham akan Yuro miliyan 101. Saidai tun wancan lokaci an samu wanda suka zarta ta da dama.

Ga 'yan wasan kwallon kafa da suka fi tsada a Duniya kamar haka:

Neymar: Barcelona ta sayarwa PSG akan miliyan 222

Mbappe: Monaco ta sayarwa PSG akan miliyan 180

Coutinho: Liverpool ta sayarwa Barcelona akan miliyan 120

Cristiano Ronaldo: Real Madrid ta sayarwa Juventus akan miliyan 112

Dembele: Dormund ta sayarwa Barcelona akan miliyan 105

Paul Pogba: Manchester United ta sayishi daga Juventus akan miliyan 105

Neymar: Barcelona ta sayoshi daga Santos akan miliyan 103

Bale: Tottenham ta sayarwa Rela Madrid akan miliyan 101

Hazard: Chelsea ta sayarwa Real Madrid akan miliyan 100

Cristiano Ronaldo: Manchester United ta sayarwa Real Madrid akan miliyan 96.


No comments:

Post a Comment