Friday, 14 June 2019

Hukumar Kwastam Na Samar Wa Da Nijeriya Naira Biliyan Biyar Da Rabi A Kullum>>Hameed Ali

A ranar Alhamis ne hukumar kwastam ta Nijeriya ta ce kudaden shigar da ta ke tattarawa a kowacce rana ya karu zuwa Naira biliyan biyar da rabi. 


Shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar aiki shelkwatar kungiyar masu sufurun kaya wadanda gwamnati ta amince wa ta kasa da ke Legas.

Shugaban kwastam din wanda ya samu wakilcin mataimakinsa mai kula da shiyar A, Kaycee Ekekezie, ya ce karin kudin shigar ya taimaka gurin biyan albashin ma'aikatan a kan lokaci tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga asusun kasa ta fuskar kudin shiga.


No comments:

Post a Comment