Thursday, 20 June 2019

Jami'ar ABU ta mayar da martani kan dalibinta daya sha tabar wiwi da shedar digirinshi

Dazune muka ji labarin yanda wani matashi yayi amfani da takardar shedar kammala digirinshi daga jami'ar Ahmadu Bello, ABU wajan shan tabar Wiwi. Jami'ar ta mayar da martani akan lamarin.Da dama sun i Allah wadai da wannan lamari inda har wani ya bayyana cewa su a jami'ar Usman Danfodio Sokoto ana la'akari halayya da kuma ilimin mutum wajan bashi shedar digiri.

Jami'ar ta shafinta na dandalin Twitter ta bayyana cewa bata ji dadin abonda ya faru ba. Amma lambobi na musamman da suka bayyana a saman shedar digitin nashi zasu bayyana ko shi wanene duk da ya rufe sunanshi kuma zasu nemoshi.


No comments:

Post a Comment