Monday, 10 June 2019

Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suke Nuna Cikar Mutum

1:- Boye talaucinka har mutane su fara tunanin kai me arziki ne 

2:- Boye damuwarka akan abinda aka yi maka har mutane su fara tunanin wannan abin bai dame ka ba

3:- Danne bacin ranka a inda aka bata maka rai har mutane su fara tunanin duk abin da za a yi maka ba zai taba damun ka ba  


4:- Yin fara'a ga kowa har mutane su fara tunanin ba ka yin fushi 

5:- Zamo na kowa har mutane su fara tunanin baka da abokin fada 

6:- Ka taimaki duk wanda kake tare da shi har mutane su dinga neman taimako a wurinka 

7:-  Ka yanka ya zamo na kowa, koda kayan kowa bai zamanto naka ba, ta haka ne mutane za su ji dadin zama da kai 

8:- Ka zamanto mai kawar da kai a kayan wani har mutane su fara tunanin rayuwar duniya ba ta dame ka ba.

Mu kasance masu hakuri da junanmu domin idan mun mutu mu samu kyakkyawan karshe.

Ya Allah kasa mu dace, Ka kums sa mu gama da duniya lafiya, amin.
Rariya.


No comments:

Post a Comment