Thursday, 27 June 2019

Kalli budurwar dan kwallon kasar Senegal da ta dauki hankula

Tauraron dan kwallon kasar Senegal, Diatta Krepin kenan a wannan hoton dake ta yawo a shafukan sada zumunta inda aka ruwaito cewa wadda suke tare da ita a hoton budurwarshi ce.Lamarain dai ya dauki hankula sosai inda wasu ke cewa kudi sune kyan da namiji, wasu matan da suka bayyana ra'ayinsu kuwa sun ce da kudi ba zasu auri wasu mazan ba.

Yanzu haka dai a wasan neman cin kofin Nahiyar Afrika da ake bugawa, Krepin ya ciwa kasarshi ta Senegal kwallo da ya kuma yana wasa da kungiyar kasar Belgium, Club Brugge.

Rahotanni dai sun bayyana cewa a shekarar 2017 kungiyar Manchester United ta kasar Ingila ta taba zawarcin Krepin.


No comments:

Post a Comment