Pages

Wednesday 26 June 2019

Ke ba kala ta bace: Trump ya gayawa wadda ta zargeshi da yi mata fyade

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya karyata zargin fyade da wata mata, E. Jean Carrol ta mai inda tace ya mata fyade tun a shekarun 1990.



Matar tace sun hadune a dakin canja kaya na wani shagon sayar da kaya a nanne yake tambayarta shawarar irin dan kamfai din da zai saiwa wata, sai ya bukaceta ta gwada, daga nanne sai yayi mata fyade.

Ta bayyana cewa bata je gurin 'yansandan ba saboda tana jin tsoron abinda ka iya jewa ya zo. Matar dai itace ta 16 data zargi Trump da yin fyade.

Saidai a nashi martanin Trump yace karyace kawai matar ta shirga mai, inda yace ita ba kalarshi bace, kuma abinda tace cewa yayi be yi ba, be yi ba.

Carrol dai tace duk wanda yawa fyade in suka fito suka fada sai ya karyata sannan ya rika musu barazana.

No comments:

Post a Comment