Thursday, 13 June 2019

Kuma dai: An kawar da yunkurin sake yin juyin mulki a Sudan

Wata majiyar Majalisar Mulkin Soji ta Wucin gadi ta Sudan ta yi ikirarin cewar an kawar da yunkurin juyin mulki da wasu sojoji sama da 70 suka yi a ranar 8 ga watan Yuni.


Wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ba ta ce, wani rukuni na sojoji da suka hada da wadanda suka yi ritaya 3 bai yi nasara ba kuma mutanen sun gudu amma an fara gudanar da bincike.

Majiyar ta ce, sojojin ba su samu goyon baya ba daga sauran cibiyoyin soji dake Sudan kuma an kama wasu jami'ai 4 da ke da hannu a lamarin tare da stare su a helkwatar rundunar sojin dake Kharotum.

Babu wata sanarwa a hukumanci da gwamnatin wucin gadi ta sojin Sudan ta fitar kan wannan batu.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment