Saturday, 15 June 2019

Kylian Mbappe ne dan wasa mafi daraja a Duniya

Bayan fitar da jadawalin 'yan wasan kwallon kafa da CIES dake saka idanu akan cinikin 'yan wasa ta yi, an ga matashin tauraron dan wasan PSG, Kylian Mbappe ne dan wasa na daya a Duniya da yafi kowane daraja/tsada.Jadawalin na kunshe da taurarin kwallon kafa 20 da suka fi tsada a Duniya inda kuma Neymar ya zo a matsayi na 17 bayan da darajarshi ta sauka da Yuro miliyan 90. Mbappe ne na daya da darajar Yuro miliyan 252. Ga dukkan alama idan PSG ta sakashi a kasuwa zata sha kudi kuma kungiyoyi da dama zasu yi zawarcinshi.

Mohamed Salah ne ya zo na 2 a jadawalin da daraja ta Yuro miliyan 219. Sai kuma Raheem Sterling da yazo na 3 da datajar Yuro miliyan 207.

Messi yazo na 4 da darajar miliyan 167 yayin da Ronaldo ya zo na 20 da darajar Yuro miliyan 118, a hakan ma ya kara daraja fiye da yanda Juventus suka sayoshi daga Real Madrid a bara sannan kuma ana ganin shekarunshi sun taimaka wajan rashin yin daraja sosai.

Gaxai cikakken jadawalin kamar haka:


No comments:

Post a Comment