Pages

Tuesday 25 June 2019

Labari me ban tsoro: Yadda Amosun ya shigo da bindigogi 1000 da harsasai miliyan 4 jihar Ogun ba a sani ba

Bai fi sauran kwana daya karshen mulkin tsohon gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya cika ba, sai ya kira Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Ogun din, Bashir Makama, ya shaida masa wata maganar da za ta jefa kowa a cikin al’ajabi da firgici.


Ya shaida masa cewa ya na boye da dubban bindigogi da milyoyin harsasai, wadanda ya jibge a wani wuri na sirri a cikin Gidan Gwamnati. Saboda haka a zo a kwashe su, ya na so zai mika su a hannun ’yan sanda.


Amosun bai goyi bayan dan takarar APC a zaben gwamnan Jihar Ogun ba, saboda ba shi ya so lashe zaben fidda gwanin jam;iyyar APC din ba.

Maimakon haka, sai ya ingiza wanda ya ke doyon baya, mai suna Adekunle Akinlade ya koma jam’iyyar APM. Amma duk da haka, bai yi nasara ba, sai Dabo Abiodun na APC ya kayar da shi.

Yayin da Amosun ya shaida wa Kwamishinan ’yan sanda Makama abin da ake ciki, nan da nan cikin gaggawa ya kira wasu manyan jami’an sa, suka garzaya sai cikin Gidan Gwamnatin Ogun.


Su na isa tuni har sun tarad da an kwaso dukkan tulin makaman nan an loda cikin wasu motoci, ana jiran isowar su.

Nan da nan a cikin gaggawa gwamna mai barin gado a lokacin, Amosun ya yi takaitaccen jawabin damka bindigogi samfurin AK guda 1000, harsasai milyan 4 da kuma falmaran, rigar nan mai hana harsashi shiga jiki har guda 1000. Sai kuma motar daukar jojoji yayin da ake dumfarar fagen fama guda daya, (wato APC).


A wurin taron damka makaman ga jami’an tsaro, Amosun ya ce ya sayo makaman ne domin kokarin magance matsalar tsaro a jihar Ogun mai yawan jama’a milyan 3,751,140 a kididdigar 2006.


Ya kara da cewa ya yi tunanin adana su a Gidan Gwamnati ne domin aka jami’an tsaro su rika amfani da su ba bisa ka’ida ba.

Kammala jawabin sa ke da wuya sai aka fitar da wadannan motocin da aka loda wa tulin makamai aka kai su hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke unguwar Elewe-Eran, cikin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Makonni hudu bayan mika wadannan makamai, manyan jami’an tsaron kasar nan na cike da mamaki da fargabar yadda gwamnan farar hula zai gina fangamemen rumbun ajiyar tulin makamai a Gidan Gwamnati.


Sannan kuma su na mamakin yadda har yanzu ba a kama Amosun an yi masa hukuncin karya dokar Mallakar Makamai Ba Bisa Ka’ida ba.

Har yanzu kuma an kasa gane ta yadda aka yi har Amosun ya sayo wadannan tulin makamai, ya shigo da su kasar nan, har kuma ya jibge su a Gidan Gwamnati na tsawon lokaci, ba tare da an gano ba.

Sai dai kuma wasu masana harkokin tsaro na zargin cewa makaman da ya mallaka din sun zarce yawan wadanda ya damka wa ‘yan sanda. Su na ganin tuni akwai wasu a hannun ‘mugun iri.’


Amosun wanda a yanzu sanata ne a karkashin APC, ya ki yarda ya amsa tambayoyin da PREMIUM TIMES ta yi masa, ballantana har a ji ta bakin sa.

Da aka tuntubi kakakin yada labaran sa mai suna Rotimi Durojaiye, sai ya ce a aika masa tambayoyin da ake so a yi wa Amosun din ta e-mail.

Kwanaki biyar bayan aikawa da sakon ta e-mail, har yau ba amo kuma ba labari.

ABIN TSORO DA FARGABA

Mahukunta da dama a manyan hukumomin tsaron kasar nan daban-daban sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Amosun ya mallaki wadannan tulin makamai ne ba tare da samun lasisin shigo da su daga ofishin Masharwacin Harkokin Tsaro Ga Shugaban Kasa ba.

Sun ce wannan ofis shi kadai ne ke da hakki da iznin bayar da lasisin shigowa da sayen makamai zuwa cikin kasar nan.


Wata babbar magana kuma ita ce, ba a bayar da iznin sai ga hukuma ko wanda ke da lasisin iznin hada-hadar makamai, wanda Amosun ko Jihar Ogun duk basu cikin jerin wadannan masu lasisin.

Kakakin Yada Labarai na Ofishin NSA, mai hakkin bada iznin shigo da makamai, bai amsa tambayar da PREMIUM TIMES ta yi masa dangane da wannan harkalla ba.

Sai dai kuma wata majiya a cikin hukumar da ta nemi a sakaya sunan ta, ta tabbatar da cewa ba a bai wa Amosun ko Jihar Ogun iznin shigo da ko bindigar harbin tsuntsaye ba.


Su ma Hukumar Kwastan ta Kasa ta tabbatar da cewa a iyar sanin ta dai ba a san ta yadda aka yi Amosun ya shigo da makaman ba.

Ta ce jami’an ta ba su tantance makaman a tashoshin ruwa ko na jiragen sama ko ta kan iyakokin kasa ba.

Hakan na nuni da cewa sumogal din makaman aka yi ta barauniyar hanya a fataucin ’yan fasa-kwauri.


Kakakin Kwastan Joseph Atta, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ko hukumar soja ko ‘yan sanda da kwastan ba su iya shigo da makamai cikin kasar nan, sai da takardar izni daga ofishin NSA.

Shigo da tulin makamai cikin kasar nan na daya daga cikin abinda ya ruruta wutar kashe-kashe da sauran fitintinu a cikin kasar nan.

Ko a cikin watan Mayu, sai da kotu ta yanke wa wasu mutane uku tsawon wa’adin shekaru 120 a kurkuku, saboda kama su dumu-dumu da harkallar makamai a Jihar Oyo.


Sannan kuma yawaitar makamai ta kara haddasa yawaitar tashe-tashen hankula a lokacin zaben 2019.

Ko a Jihar Ogun din, an kashe mutane da dama a lokacin zaben shugaban kasa da na gwamna, a ranakun 23 Ga Fabrairu da 9 Ga Maris.

Lokacin sa Amosun ya zama gwamna cikin 2011, ya yi kuka dangane da yawaitar makamai a jihar, har ya kafa kwamiti, tare da zargin gwamnan da ya gada, Gbenga Daniel.

Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa ta ki yin magana a kan wannan badakalar makamai.

Kakakin su Frank Mba ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa idan ta na da tambaya, ta yi wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Bashir Makama.

Makama shi ne wanda tsohon gwamna kuma sanatan APC a yanzu, Ibekunle Amosun ya damka makaman a hannun sa, sa’o’i kadan kafin ya sauka daga mulkin jihar Ogun.


No comments:

Post a Comment