Thursday, 6 June 2019

Lamarin Kano ya zama abu na daya da aka fi tattaunawa da daukar hankali a shafin Twitter

Bayan fitar da sanarwar soke hawan hawan Nasarawa da gwamnatin jihar Kano ta yi bisa uzurin ayyuka sun wa gwamnan yawa da kuma matsalar tsaro 'yan najeriya da dama sun hau shafin twitter inda suka rika yin sharhi akan batun.Lamarin na Kano ya zama abu na daya da aka fi tattaunawa akanshi a Twitter.

Gwamnan ya halarci hawan Sallar da aka yi a masarautar Bichi. A hawan sallar da aka yi a Kano ya kare ba dadi inda aka samu rikici wanda yayi sanadin mutuwar mutum daya da kuma jikka ta wasu biyu, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu na ganin cewa abinda ke faruwa tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar ya zama kamar wasan yara.

A ra'ayin wani yana ganin kamata yayi manyan Arewa su saka baki a wannan rashin jituwar dan duk abinda ya taba Kano ya taba gaba dayan Arewa.

Wata kuma na ganin cewa da wannan abin dake faruwa gara ace gwamnan ya sauke sarkin kawai.No comments:

Post a Comment