Wednesday, 5 June 2019

Lauyoyin da suka tsayawa matar dake zargin Neymar da Fyade sun janye daga lamarin bayan zarginta da magana biyu: Mahaifiyar Neymar din tace ya yafewa matar

Lauyoyin da suka tsayawa matarnan da ta zargi Tauraron dan kwallon Brazil me bugawa PSG wasa, Neymar da yi mata fyade sun janye daga tsaya mata da suke saboda magana biyu da suka ce ta yi akan lamarin.Lauyoyin sunce matar da ba'a bayyana sunanta ba ta gaya musu cewa sun fara jima'i na yadda da juna ita da Neymar amma daga baya sai ya sa mata karfi yayi kamar fyade.

Saidai a rahoton da ta baiwa 'yansanda matar tace gaba daya Neymar din fyadene ya mata.

Sunce da wannan dalili yasa suka yanke shawarar janyewa daga lamarin.

Bayan bayyanar wannan labari ne sai mahaifiyar Neymar din ta bayyana mai cewa tunda dai gaskiya ta fara bayyana ya yafewa matar kasafin da tamai ya fuskanci abinda yafi mai muhimmanci a rayuwa, watau Kwallon kafa.

Mahaifiyar ta Neymar tace ya lura da cewa su kiristane ya yafe wa matar ya rumgumi Yesu.

No comments:

Post a Comment