Tuesday, 11 June 2019

Mabiyan Adam A. Zango sun kai miliyan 1 a Instagram

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya shiga sahun taurarin Kannywood da suka samu mabiya miliyan 1 a dandalin Instagram. Adamun ya bayyana farin cikin shi da hakan inda ya bayyana cewa idan babu masoyanshi babu shi.Muna tayashi murna.

Kafi  Adamun akawai irin su Rahama Sadau, Hadiza Gabon, Ali Nuhu, Fati Washa da Nafisa Abdullahi da suka samu mabiya miliyan 1 a dandalin na Instagram.

No comments:

Post a Comment