Sunday, 9 June 2019

'Madrid ta kawo Hazard ne ya maye mata gurbin Ronaldo'


Eden Hazard
Bayan tabbatar da komawar tauraron dan kwallon Chelsea, Eden Hazar Real Madrid, abinda ya fi daukar hankali kuma ake ta tattaunawa akanshi shine ko dan wasan zai iya maye gurbin tsohon tauraron kungiyar, Cristiano Ronaldo?

Wasu dai na ganin ko kusa Hazard ba zai iya maye gurbin irin rawar da Ronaldo ya takawa Madrid ba, wasu kuwa na ganin zai iya.

A hirar da Sky Sports ta yi da wani tauraron me sharhi akan harkar kwallon kafa me suna  Kristof Terreur da ya fito daga kasar Belgium wanda Shima Hazard din dan kasarne ya bayyana cewa yana tsammanin Hazard din zai buga wasa a bangaren hagu ne a kungiyar Madrid kamar yanda yakewa Chelsea. Ya kara da cewa zai iya tuna tun a shekarar 2016 ne wakilan Real Madrid suka fara tattaunawa da wakilan Hazard inda a wancan lokacin suka bayyana cewa suna bukatar dan wasanne ya zama madadin Ronaldo.

Yace to saidai be san watakila ko yanzu su canja ra'ayi akan inda zasu ajiye Hazard din ba.

Lokaci dai be bar komai ba.

No comments:

Post a Comment