Friday, 14 June 2019

Magori wasa kanka da kanka:Ba zan taba mantawa da nasarorin dana samu a shekarar 2019 ba>>Ronaldo

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya godewa masoyanshi sannan kuma ya bayyana irin nasarar da ya samu a shekarar 2019.
A sakon da ya fitar ta shafinshi na Instagram, Ronaldo ya saka hotunan kofunan da ya dauka a 2019 sannan ya rubuta cewa, kakar wasace da bazan taba mantawa da ita ba, da kuma babbar kungiya, gari me dadin sha'ani ga yanayi me kyau. Na kafa tarihi na kuma dauki kofuna har 3.

Dolene in godewa dukkan masoyan kungiyar Juventus lura da yanda aka tarbe ni a Italiya kun taimaka sosai wajan nasarar da muka samu. Ina godiya ga masoyana na Duniya baki daya musamman 'yan kasata ta Portugal da suka taimaka muka samu wata nasara me cike da tarihi. A koda yaushe ina sonku.

Ya kara da cewa, bazan taba mantawa da tarihin dana kafa ba da kuma nasarorin dana samu a wannan shekarar ba.
Misali: Ni naci kwallon da ta bamu nasara muka dauki kofin Italian Super Cup.
Daukar kofin Seria A, da kuma zama tauraron gasar da kuma cin kwallaye 21.
Cin kofin Nations Cup na turai da kuma cin kwallaye 3 da na yi a wasa daya(Hat-trick).
Na kasance dan kwallon kafa na farko da ya samu nasara a wanni 100 dana buga da kuma cin kwallaye 125 a gasar Champions League.
Na zama dan kwallo na farko da ya dauki kofunan Uefa 10 a tarihi.
Na zama dan kwallo na farko da ya ci kwallo a kowane wasan zagaye na karshe da kasarshi ta kai.No comments:

Post a Comment