Tuesday, 25 June 2019

'Malami ya yi wa yarinya fyade a masallaci' a Legas


Wata kotu a birnin Legas na Najeriya ta bada umarnin a ci gaba da tsare wani "malamin addinin Musulunci" bayan da aka tuhume shi da laifin yi wa wata yarinya fyade a wani masallaci.

Alkalin kotun ya amince da bukatar mai shigar da kara na a ci gaba da tsare Abdulsalam Salaudeen, sannan ya dage cigaba da shari'ar zuwa 14 ga watan Okotoba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa ana tuhumar Mr Salaudeen, mai shekara 43, da laifin lalata yarinyar, wacce take karkashin kulawarsa.


Sai dai mutumin da ake tuhuma ya musanta aika ba daidai ba.

Mai shigar da kara T. Olanrewaju-Dawodu, ya shaida wa kotun cewa Mr Salaudeen ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Disamba na 2018, a harabar masallacin Olorunbabe da ke lamba 15, a kan hanyar Palace Road, Igando, da ke kusa da birnin Legas.

Olanrewaju-Dawodu ya kara da cewa Mr Salaudeen, wanda aka fi sani da Alfa, an kama shi ne yana aikata laifin bayan da aka sanya kamarar daukar hoto ta sirri a masallacin domin hakon masu laifi.

Masu gabatar da kara sun ce laifin ya sabawa sashi na 137 na dokar Aikata Laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment