Pages

Wednesday 26 June 2019

Mara lafiyane jirgin sama ya dauka a yayin tsaikon ababen hawa ba shahararren me kudi ba

Labarin wani jirgi da ya dauki wani a kan titin Ore da ya hada birnin Legas da Benin ya dauki hankulan 'yan Najeriya sosai inda aka ruwaito cewa wani hamshakin attajirine da tsaikon motoci ya isheshi ya kira jirgi me saukar Angulu ya daukeshi, saidai an gano gaskiyar labarin cewa ba haka bane.



Me kamfanin Jirgin ya shaidawa BBC cewa mara lafiyane jirgin yaje dauka ba wani me kudi ba. Yace mara lafiyar na fama da matsalar hawan jini inda kuma ciwon shanyewar jiki ya sameshi shine suka kawo mai dauki

Ya kara da cewa suna amfani da jirginne wajan kaiwa ga guraren da ake bukatar taimakon gaggawa kuma wannan ba shine karin farko ba.



No comments:

Post a Comment