Thursday, 13 June 2019

Masarautar Kano: Ganduje Ya Gindaya Sabbin Sharudda Kafin Ya Yi Sulhu Da Sarkin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana sabbin sharudda kafin ya yi sulhu da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.


Gwamnan ya nemi Sarkin Kano da ya fito fili ya nemi afuwarsa da ta mutanen Kano a kan "jan kima da darajar masarautar Kano cikin kazantar siyasa". 

Gwamnan ya kuma bukaci Sarkin da ya janye dukkan kararrakin da aka shigar gaban kotu masu kalubalantar yunkurin kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano. 

Dadin-dadawa, Sarkin kuma ya rungumi sarakunan masarautun Rano, Karaye, Gaya da Bichi hannu biyu-biyu, tare da amfani da dukiyarsa da kwarewarsa gurin jagorantarsu gurin bunkasuwar jihar Kano.

Gwamnan, ta yawun tsohon kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya ce matukar Mai Martaba Sarkin ya cika wadannan sharuddan, to za su yi sulhu.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment