Thursday, 27 June 2019

Mata 3 sun zargi tsohon shugaban kasar Gambia, Yahaya Jammeh da musu fyade

Rahotanni daga kasar Gambia na cewa, mata har 3 sun fito sun zargi tsohon shugaban kasar, Yahaya Jammeh da yi musu fyade a zamanin da yake mulki.Rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Humran Right Watch da wata kungiya itama ta kare hakkin dan adam ta kasar Switzerland suka fitar ya bayyana cewa wasu mata 4 da wani tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasar sun bayar da sheda akan zargin fyaden.

Rahoton ya kara da cewa, Yahaya Jammeh yakan zabi matan da yake so a kawo mai ya musu fyade sai ya basu kudi ko kuma kyautar wani abu ko kuma ya rika wa iyalansu ihisani ko kuma ya dauki nauyin karatunsu har zuwa kasashen waje.

Zaka so karanta: An tirsasawa dan shekaru 14 auren budurwarshi data girmeshi bayan da ya dirka mata ciki


Rahoton yace yakan ajiye matanme a kusa da fadar shugaban kasa ta yanda daya bukacesu saidai a kawo mai su kuma akwai wasu mata 'yan uwanshi dake taimakamai wajan zabo  'yan matan da ya rika wa fyaden.

Daga cikin wanda suka zargeshi da fyaden akwai wata wadda ta lashekyautar sarauniyar kyau ta kasar, Toufah Jallow wadda a wancan lokacin tana 'yar shekaru 18.

A lokacin wata saukar karatun Qur'ani da aka yi a fadar gwamnatin ya bukace ta amma ta ki amince mai sai ya sa aka ajiye mai ita a wani daki ya rika mata barazana hadda duka amma ta kiya. Har tayin aure ya mata amma taki amincewa.

Saida ya mata allura sannan ya samu ya mata fyade. Bayan ta kubuta shine ta gudu zuwa kasar Senegal.


No comments:

Post a Comment