Sunday, 9 June 2019

Maza miliyan 115 suka yi aure suna yara>> UNICEF

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce akalla yara miliyan 115 ne suka yi aure suna yara a duniya.


A cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar ta ce ana aurar da yaro daya cikin biyar kafin cika shekara 15.

Rahoton UNICEF ya yi nazari ne kan kasashe 82, kuma binciken ya ce an fi yin auren wuri tsakanin maza a kasashen Afirka da ke kudu da sahara da Latin Amurka da yankin Caribbean, da kudanci da gabashin da kuma yankin Pacific.

"Aure na sace kuriciya," in ji babbar daraktar hukumar Henrietta Fore.

Ta ce ana tursasawa maza daukar nauyin da girmansu bai ba wanda kuma ba su shirya ba.

"Auren-wuri shi ne zama magidanci da wuri, wanda ke kara nauyi kan mutum musamman wajen samar da abinci ga iyali wanda kuma ke takaita wasu damammaki na samun ilimi da aikin yi."


Alkalumman binciken sun ce kasar Afirka ta tsakiya ce aka fi aurar da maza da wuri, sai kuma Nicaragua da Madagascar.

Sabbin alkalumman hukumar sun ce jimillar yara mata da maza miliyan 765 aka yi wa auren wuri a duniya.

Mata ne matsalar ta fi shafa a cewar rahoton, inda ake aurar da mace daya cikin biyar kasa da tsakanin shekara 20 zuwa 24 kafin su cika shekara 18, ake aurar da su, idan aka kwatanta da alkalumman maza daya cikin 30 da ake yi wa auren wuri.

UNICEF ta ce wannan ne rahoto na farko game da gano alkalumman adadin yawan auren wuri tsakanin yara maza.

Hukumar ta ce auren wuri ya sabawa yarjejeniyar da aka amince ta kare hakkin yara kanana, kuma yawanci 'ya'yan talakawa ne matsalar ta fi shafa wadanda ke fadi-tashin samun abin da za su ci kuma su kara dora wa 'ya'yansu wahala.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment