Thursday, 13 June 2019

Messi ya fi kowanne dan wasa kudi a Duniya

Dan wasan Barcelona dan asalin kasar Argentina, Lionel Messi, shi ya fi kowanne dan wasa karbar albashi a duniya, inda a cikin watanni 12 da suka gabata, ya samu Dala miliyan 127, kwatankwacin Nairar Najeriya biliyan 45 da miliyan 720 kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.Dan wasan Portugal da ke taka leda a Juventus, Cristiano Ronaldo ne ke a matsayi na biyu wajen samun kudi,inda ya samu Dala miliyan 109, kimanin Nairar Najeriya biliyan 39 da miliyan 240.

Mujallar ta bayyana Neymar na Brazil da ke taka leda a PSG a matsayi na uku,inda ya samu Dala miliyan 105.

‘Yar wasan kwallon Tennis, Serena Williams, ita ce mace daya tilo da ta shiga sahun ‘yan wasa 100 da ke kan gaba wajen samun kudin,inda take da Dala miliyan 29.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment