Thursday, 27 June 2019

Miliyan 15 kuke karba duk wata: Itse Sagay ya mayarwa da Ahmad Lawal martani

Farfesa itse Sagay wanda shine shugaban kwamitin dake baiwa shugaban kasa shawara akan yaki da rashawa da cin hanci ya bayyana cewa maganar albashi da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawal yayi na cewa 750,000 suke dauka a wata akwai kokarin kawar da hankalin 'yan Najeriya akai.Sagay yace yana girmama Lawal amma maganar gaskiya ba iya abinda ake biyansu kenan ba. Yace Eh a zahirin gaskiya iya albashinsu kenan amma 'yan majalisar na kwasar garabasane ta wajan alawu-alawus da ake biyansu, kamar na kayan daki da ofis, tafiye-tafiye dadai sauransu.Sagay ya kara da cewa, a wata kowanne dan majalisa na tashi da miliyan 15 idan aka tattara komai dan haka Lawal tsagoran albashin kawai ya fada.

Yace abinda bai tabbatar ba shine albashin shuwagabannin majalisar saboda su nasu kudin dabanne, abinda suke karba yana kai miliyan 280 a shekara, watau kwatankwacin miliyan 23 kenan duk wata, kamar yanda Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment