Friday, 14 June 2019

Miliyan bakwai ta bata a gidan zoo a Kano

Jami'an kula da gidan namun daji na zoo da ke Kano sun ce suna bincike kan naira miliyan bakwai da ta yi batan dabo.


Mutane a kafafen sadarwa na zamani na ta yada labarin da zargin cewa wani goggon biri ne ya cinye kudin.

Shugaban gidan zoo din Umar Kashekobo ya ce: "'Yan sanda na bincike kan ainihin abin da ya faru - abin da zan iya cewa kawai shi ne kudi sun bata."

Mai magana da yawun 'yan sandar jihar Abdullahi Kiyawa ya ce kudaden shiga gidan zoo din na kwana biyar ne suka yi batan dabo.

Ya shaida wa BBC cewa zuwa yanzu an kama mutum 10 kuma jami'ai na binciken abin da ya sa ake ajiye kudi mai yawa haka ba tare da kai su banki ba.

A farkon makon nan gidan rediyon Freedom a Kanon ya sanar da bacewar kudin.

A bara ma hukumomin gidan zoo din sun ce kudi ya bata bayan da aka gama hada-hadar hidimar sallah, wanda shi ne lokacin da aka fi samun cinikin shiga gidan.

A shekarar da ta gabata ma wata ma'aikaciya a hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta Jamb reshen jihar Benue, ta ce wani maciji ya shiga ofishin ya hadiye naira miliyan 36 kudin jarabawar da aka tara.

Makonni kadan da suka gabata ita da wasu jami'an suka musanta hannu a batan kudin.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment