Friday, 14 June 2019

Na yi farinciki da majalisar dinkin Duniya ta shaida cewa ina yaki da rashawa da cin hanci da kuma kawar da yunwa>>Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikin shi da ganin cewa majalisar dinkin Duniya ta shaida kokarin da yake wajan yaki da rashawa da cin hanci da kuma kawar da talauci a Najeriya.Shugaba ya bayyana hakane a ganawar da yayi da wakilin sakataren majalisar dinkin Duniya, Muhammad Ibn Chambas a fadarshi.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa dangantaka me kyau tsakanin kasashe makwabtan Najeriya zai taimaka wajan yaki da 'yan ta'adda.

Chambas wanda shine ya wakilci sakataren majalisar dinkin Duniya a bikin ranar Dimokradiyya ya bayyana cewa, sakataren ya yaba da gaskiya da kuma yanayin shugabancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, musamman ta bangaren yaki da cin hanci da kuma ganin an gudanar da ayyukan gwamnati yanda suka kamata.

Ya kuma ce MDD ta yabawa Najeriya wajan yaki da talauci da yaki da 'yan ta'adda da kuma kokarin dawo da tafkin Chadi da ya kafe.

Ya kuma yaba da zabar wakilin Najeriya na dindindin a majalisar dinkin Duniya a matsayin shugaban majalisar inda yace abokan aikinshi a New York sun matukar girmamashi kuma zasu tabbatar da ganin cewa yayi shugabanci me kyau ta yanda zai kaaance abin alfahari ga Najeriya da Afrika gaba daya.

No comments:

Post a Comment