Wednesday, 12 June 2019

Najeriya na fuskantar mawuyacin hali karkashin mulkin Buhari>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya bayyana cewa kasar na tunkarar wani mawuyacin hali karkashin mulkin Buhari.Obasanjo ya bayyana hakane a wata hira da yayi da jaridar Premium Times inda ya bayyana cewa shugaba Buhari ya lalata tattalin arzikin kasarnan sannan yaki da rashawa da yace yana yi shima lalatashi yayi maimakon gyara. Obasanjo wanda shine ya kirkiro hukumomi 2 na EFCC da ICPC dake yaki da rashawa a kasarnan ya bayyana cewa Buhari ya lalata aikin hukumomin kuma Najeriyar na ci gaban me hakar rijiyane.

Ya kara da cewa kuma abin mamaki shine yanda manyan masu rike da mukamai 3 na kasarnan duk daga Arewa suke amma Buharin be damu ba,  saboda yana fifita mutanenshi akan sauran 'yan Najeriya.

Obasanjo ya kara da cewa, Buhari, babban alkalin alkalai na kasa da kakakin majalisar dattijai duk daga Arewa suke amma Buhari be damu ba.

No comments:

Post a Comment