Pages

Wednesday 26 June 2019

Najeriya ta kai mataki na gaba a gasar Nations Cup: Ta lallasa Guinea da ci 1-0

Najeriya ta lallasa kasar Guinea a wasan da suka buga yau da ci 1-0 a ci gaba da gasar neman daukar kofin Nations Cup da ake bugawa a kasar Egypt.



Kenneth Omeruo ne ya ciwa Najeriya kwallonta a yayin da ake mintuna 73 da wasa.

Najeriya dai ta kasance kasa ta farko data tsallake zuwa mataki na gaba a gasar inda kasashe 16 zasu buga wasan neman kaiwa matakin kusa dana kusa dana karshe.


No comments:

Post a Comment