Sunday, 9 June 2019

Portugal ta lashe kofin Nations Cup na turai: Silva ya kafa tarihi

Kasar Portugal ta lashe kofin Nations Cup na kasashen Turai bayan lallasa kasar Netherlands da ta yi da ci 1-0 a wasan karshe da suka da yammacin yau. Goncalo Guedes ne ya ciwa Portugal kwallonta bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.An yi tsammanin taurarin kwallo, Cristiano Ronaldo da Virgil Van Dijk ne zasu dauki hankula a wasan sai dai lamarin ya canja bayan da  Guedes da Silva suka fi daukar hankali.

Portugal ta kai hari har sau 11 saidai ita kuma Netherlands sau daya tal ta kai hari gidan Portugal.

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa Manchester City wasa, Bernardo C Silva yayi bajinta sosai inda a kakar wasa ta bana ya daga kofuna 5, Premier League, da Community Shield, da FA Cup, League Cup, da Uefa Nations League, sannan kuma shine gwarzon dan wasan Manchester City na kakar wasan 2018/19, kuma shi aka baiwa gwarzon dan wasan gasar ta Uefa Nations Cup, ya ci kwallaye 14 ya bayar da taimako an ci 11.


No comments:

Post a Comment