Monday, 17 June 2019

PSG na son sayar da Neymar


Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta PSG a shirye take ta sayar da tauraraon dan kwallonta, Neymar idan ta samu ta yi me kyau.

Rahoton L’Équipe yace PSG na son sayar da Neymar ne saboda yanda sunanshi ya baci saidai kungiyar ba zata sayar dashi kasa da yanda ta siyoshi daga Barcelona ba watau Yuro miliyan 222.

Hakanan L’Équipe tace Neymar din ma ya gayawa wasu makusantanshi cewa yana son barin kungiyar.

Jaridar ta kuma tabbatar da cewa, tuni aka fara tattaunawa tsakanin Barcelona da PSG akan komawar dan wasan tsohuwar kungiyarshi wanda kuma a cinikin Barca zata baiwa PSG wani dan wasanta sannan ta mata ciko da kudi akan farashin Neymar din.No comments:

Post a Comment