Friday, 14 June 2019

Ramos zai yi aure, ya gayyaci taurarin 'yan kwallo amma bai gayyaci Ronaldo ba


Rahotanni daga Sifaniya na cewa tauraron dan kwallon Real Madrid, Sergio Ramos zai angwance in da zai auri budurwarsa, Pilar Rubio wadda tauraruwar me gabatar da shirye-shiryece a gidan talabijin a karshen makonnan me zuwa. Abu mafi daukar hankali dangane da bikin shine Ramos ya gayyaci abokan aikinshi na da dana yanzu amma bai gayyaci Cristiano Ronaldo ba.

Rahotanni daga Marca sun ce Ramos ya gayyaci taurarin 'yan kwallon Barcelona irin su Gerrard Pique da David Beckham amma bai gayyaci Ronaldo ba da suka shafe shekaru 9 suna kwallo tare ba.

Da ma dai rahotanni sun bayyana cewa kamin barin Ronaldo daga Madrid ya samu sabani da Ramos.

Sauran wadanda Ramos din ya gayyata a wajan auren nashi sun hada da Luka Modric, Zinedine Zidane, Jordi Alba, Sergio Busquets, Fernando Hierro, Ronaldo Nazario, Roberto Carlos, Vicente del Bosque, Iker Casillas, Shakira da Victoria Beckham.

No comments:

Post a Comment