Friday, 14 June 2019

Rashin halartar tsaffin shuwagabannin kasa mayan taruka alamace dake nuna cewa akwai matsala tattare da shugaba me ci>>Sanata Shehu Sani


Tun ranar da aka rantsar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zango na biyu na mulkinshi a ranar 29 ga watan Mayu, tsohon shugaban kasa Yaukubu Gowon ne kawai ya halarci bikin cikin tsaffin shuwagabannin Najeriya.

Hakanan a ranar Dimokradiyya ta Yuni 12 babu ko daya daga cikin tsaffin shuwagabannin Najeriyar da ya halarta. Hakan na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankula a ranar.

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa, idan kaga tsaffin shuwagabannin kasa na kauracewa manyan tarukan kasa to zakasan cewa akwai matsala da gwamnati ko kuma shugaba me ci ke dashi. Idan ma za'a iya tuna tarihi suma sun kwaikwayi shugaban me ci ne.

No comments:

Post a Comment