Wednesday, 12 June 2019

Real Madrid ta bayyana Luka Jovic a matsayin dan wasanta

A yau, Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana sabon dan wasan ta da ta sayo, Luka Jovic daga kungiyar Eintracht Frankfurt a filin wasanta na Santiago Bernabeu. Shugaban kungiyar Florentino Perez ne ya jagoranci gabatar da Jovic.Da yake hira da manema labarai, Jovic ya bayyana cewa shine matashi mafi farin ciki a wannan rana Sannan ya san cewa zuwa Madrid da yayi shawarace me kyau wadda ba zai yi dana sanin yinta ba.

Ya kara da cewa zai yi dukkan mai yiyuwa wajan taimakawa kungiyar ta kai gaci a kakar wasa me kamawa.

Da aka tambayeshi, wane dan wasan Real Madrid ne gwaninshi? Sai ya kada baki yace, lokacin yana karamin yaro, Cristiano Ronaldo ne gwaninshi amma yanzu bashi da gwani, zai yi wasa tare da kowa.

Ya kuma tabbatar da wata magana da Shugaban Madrid din, Perez yayi na cewa lokacin yana yaro yana yin bacci da rigar Real Madrid a jikinshi, inda yace wani dan uwanshine ya baahi kyautar rigar dan haka baya son rabuwa da ita lokacin yana yaro.


No comments:

Post a Comment