Thursday, 13 June 2019

Real Madrid ta dauki Ferland Mendy

Real Madrid ta dauko dan kwallon Olympique Lyon, Ferland Mendy.


Mendy ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara shida, wadda za ta kare a karshen kakar 2025.

Real Madrid ta dauko dan wasan ne kan kudi fam miliyan 47.1, kuma jumulla kungiyar ta kashe kusan fam miliyan 300.


Real din ta dauki dan wasan Belgium, Eden Hazard daga Chelsea kan kudi da ya kai sama da fam miliyan 150 da dan kwallon Serbia, Luka Jovic daga Eintracht Frankfurt kan kudi fam miliyan 53.

A kuma watan Maris Real Madrid ta sanar da daukar dan kwallon Porto, Eder Militao kan kudi fam miliyan 42.7.

Real za ta gabatar da Mendy gaban magoya bayanta ranar Laraba 19 ga watan Yuni a Santiago Bernabeu.

A ranar ake sa ran Mendy zai taka filin wasa na Santiago Bernabeu a karon farko dauke da rigar Real Madrid, daga nan ya gana da 'yan jarida.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment