Thursday, 13 June 2019

Real Madrid ta gabatar wa da masoyanta Eden Hazard a matsayin sabon dan wasanta saidai sun yi ta fadin cewa Mbappe Suke so


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a yau, Alhamis ta gabatar da tauraron dan kwallon da ta sayo daga Chelsea, Eden Hazard ga magoya bayan kungiyar a filin wasanta na Santiago Barnabeu.Hazard ya bayyana farin cikinshi sosai da zama dan wasan Real Madrid inda yace sanannen abune tun yana karamin yaro Zidane ne tauraron dan wasanshi kuma yanzu gashi shine kocin Real Madrid sannan kuma gashi kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d' Or tana kungiyar ta Real Madrid a hannun Luka Modric, yace watakila a Real Madrid an fi samun damar cin kyautar amma dai zai gwada ya gani, saidai ya kara da cewa abu mafi muhimmaci shine wasan da zasu buga tare da sauran 'yan kwallon kungiyar dan cin kofuna.

Hazard ne babban dan wasan da kungiyar ta sayo tun bayan Gareth Bale data siyo a shekarar 2013 daga kungiyar Tottenham sannan kuma shine dan wasan da magoya bayan kungiyar suka fi fitowa da yawa dan kallonshi a ranar farko da aka gabatar dashi tun bayan Cristiano Ronaldo. Mutane dubu 70 ne suka fito kallon Ronaldo saidai mutane dubu 50 ne suka zo kallon Hazard a yau.

Hazard yace kyaftin din Madrid( Ramos) ya iya buka kwallon daga kai sai Gola amma idan zai bashi dama, zai so ya zama me buga irin wannan kwallon. Ya kuma ce zai so ya buga wasa a bangaren hagu ko kuma lamba 10 a kungiyar.
Saidai wani abu daya dauki hankula a lokacin gabatar da Hazard din shine yanda magioya bayan Real Madrid din da suka taru suka rika fadin cewa'Mbappe muke so'. Wannan abu ya dauki hankula sosai inda wasu da dama suka yi Allah wadai da hakan ganin cewa lokacine da ake gabatar da Eden Hazard kuma maganarshi ya kamata a yi ba ta wani dan kwallon ba.

Saidai bayan da Hazard ya sumbaci tambarin Real Madrid sai gaba dayan filin ya kaure da sowa.
No comments:

Post a Comment