Wednesday, 19 June 2019

Real Madrid ta sake sayen wani dan wasan gaba


Rodrygo kisses the Real Madrid badge during his presentation.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kara shiryawa kakar wasa me zuwa inda da ta dukufa wajan sayen 'yan wasa ba kama hannun yaro. A jiyane, Talatane kungiyar ta sayo tauraron dan wasan kungiyar Santos kuma dan asalin kasar Brazil, Rodrigo Silva Goes.

Rodrigo dai ya zama dan wasan gaba na uku kenan, bayan Eden Hazard, da Luka Jovic da Real Madrid ta siya a wannan kakar.

A yanzu dai kungiyar ta Real Madrid na da 'yan wasan gaba guda 11 kenan da suka hada da Karim Benzema, Gareth Bale, Marco Asensio, Mariano Diaz, Vinicius Junior, Brahim Diaz, Lucas Vazquez da kuma Borja Mayoral. Idan aka hada da sabbin 'yan kwallo 3(da aka lissafa a sama) da Marid ta sayo su 11 kenan.

Wasu masu sharhi na ganin cewa yawancin su Madrid din zata bayar da su aro ne.

Dama dai kocin Madrid, Zidane a lokacin da ya dawo kungiyar ya bayyana cewa kungiyar na kamfar cin kwallaye duk da kwallaye 30 da Benzema ya ci, dalili kenan da yasa da aka bude kasuwar cinikin 'yan wasa kungiyar ta mayar da hankali wajan sayen 'yan wasan gaba.

Rodrigo ya bayyana cewa, ba ya son yayi irin wasan Neymar a Madrid, zai yi irin wasanshine da ya saba yi.

Wani rahoto da yayi ta yawo a kafafen watsa labarai game da sabon dan wasan na Real Madrid shine amincewa da yayi ya koma Madrid cikin doki.

Rahoton yace cikin mintuna 20 da fara tattaunawa da dan wasan ya mince ya koma Madrid. Madrid ta biya Yuro miliyan 45 akan sayen dan wasan. kuma shima da aka tambayeshi akan haka sai ya kada baki yace:

Duk wanda ya sanni tun ina yaro ni masoyin kungiyar Real Madrid ne kuma na sha gayawa babana cewa wata rana sai na bugawa kungiyar wasa dan haka da suka zo maganar sayena ban tsaya wata jayayyaba

No comments:

Post a Comment