Saturday, 8 June 2019

Real Madrid ta tabbatar da sayen Eden Hazard daga Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da sayen tauraron dan kwallon Chelsea, Eden Hazard akan Fan miliyan 130 inda zai yi shekaru 5 a kungiyar kamar yanda kwantirakin sayen nashi ya nunar wanda zai tabbata bayan an kammala mai gwajin lafiya.Sky Sport ta tabbatar da cewa a ranar 13 ga watan Yuni ne Madrid din a hukumance zata gabatar da Hazard a matsayin dan wasanta.

Shima a nashi bangaren, Hazard ya bayyana a shafinshi na Twitter cewa, yanzu dai kunsan zan koma Real Madrid, na kasance ina da burin buga musu wasa tun ina dan karamin yaro.

Amma duk da haka barin Chelsea ba karamin abubane a gareni, yayi fatan farantawa Magoya bayan Madrid a wasan da zai bugawa kungiyar.

Hazard ya bugawa Chelsea wasanni 352 inda yaci kwallaye 110 da kuma bayar da taimako aka ci kwallaye 92 sannan yaci kofuna 6

No comments:

Post a Comment