Monday, 10 June 2019

Ritayar Onnoghen: Matakin da Buhari ya dauka 'abin takaici ne'

Masu fafutuka sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na amincewa da yin ritayar tsohon babban alkalin kasar, Walter Onnoghen, suna cewa babban nakasu ne ga yaki da cin hanci da rashawa.


A ranar Lahadi ne shugaban ya amince da ritayar Walter Onnoghen, wanda aka dakatar, sannan kotun da'ar ma'aikata ta samu da laifin kin bayyana cikakkun kadarorinsa.

Wannan mataki abin "takaici ne, kuma na nufin kamar an yafe masa laifinsa ne", a cewar lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Audu Bulama Bukarti.

Babu wani cikakken bayani kan dalilin da ya sa shugaban ya amince da ritayar, sai dai tuni Majalisar Kula da Alkalai ta kasa (NJC) ta yi marhabin da matakin nasa.

Wannan mataki da Buhari ya dauka na nufin Mista Onnoghen zai karbi dukkan garabasar da ma'aikata ke karba idan sun yi ritaya duk da laifin da aka same da shi.

Makudan kudade alkalan kasar ke samu bayan sun kammala aiki.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment