Thursday, 6 June 2019

Ronaldo ya ci Hat-Trick ta 53 a wasan da Portugal ta buga da Switzerland

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya zazzaga kwallaye 3 wanda a turance ake kiransu da Hat-rick a wasan da suka buga a yammacin jiya da kasar Switzerland wanda wannan ya basu damar zuwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun kasashen turai.Ronaldo ya fara cin kwallo da wani kayataccen Free-kick inda Switzerland suka rama kwallon saidai ba'a tashi wasan ba saida Ronaldo ya bayyanawa Switzerland cewa be gama basu mamaki ba inda ya kara zura kwallaye 2 a ragarsu. An tashi wasan da sakamakon 3-1, Portugal na cin Switzerland.

Wannanne Free-kick na 53 a tarihin buga kwallon Ronaldo inda ya ciwa Real Madrid guda 44 sannan ya ciwa kasarshi ta portugal guda 7 sai kuma Manchester United da Juventus da ya ciwa kowannen su 1. Da dama sun jinjinawa dan kwallon ganin cewa ya fara tsufa a Duniyar Kwallo, watau shekarunshi 34 amma har yanzu yana cin irin wadannan kwallayen na ban mamaki?

A tarihin kasar Portugal basu taba kaiwa wasan karshe na wata gasar kasashen turai ba saidai a karkashin Ronaldo sun je wasannin karshe na gasar kasashen turai har sau 3.

Yanzu dai Ronaldo ya ci kwallaye 689 kenan a tarihin buga kwallonshi, Hat-tricks guda 53, ya ciwa kasarshi kwallaye 88. 

No comments:

Post a Comment