Wednesday, 12 June 2019

SAKIN MAHAIFIYA YA JANYO YARINYA TA KASHE KANTA A KANO


Wata yarinya 'yar shekara 17, Sadiya Shehu daga unguwar Tudun Murtala, karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano ta kashe kanta sakamakon sabanin da ya shiga tsakanin mahaifanta wanda ya janyo saki ya shiga tsakani. 

Sadiya ta rasa ranta a ranar Litinin sakamakon shan maganin kashe kwari da ake kira fiya-fiya, wanda mahaifiyarta ta aje a dakinta domin kashe sauro da sauran kwari. 

Da yake magana da jaridar Chronicle, mahaifin mamaciyar, Malam Shehu A Lawan ya tabbatar da cewa Sadiya ta kashe kanta sakamakon 'yar karamar matsala da ta faru a tsakanin shi da mahaifiyarta a ranar Lahadi wadda a cewarsa daga baya sun shirya a ranar.

Amma a nata bangaren, Malama Amina Shehu, wadda take mahaifiya ga mamaciyar cewa ta yi rikicin ya fara a lokacin da wata Maryam, wadda mijin nata yake kawu a gurinta, take dukan kanin mamaciyar. Ganin haka ya sa shi ma mijin nata ya taso ya fara dukan yaron.

“Maryam ce ta shigo ta fara fada da dana Dadi a kan wai ya zage ta. Da mahaifinsa ya fito daga bandaki sai kawai ya rufe shi da mugun duka. Ni kuma na gaza jurewa. Sai na gaya masa hukuncin ya yi tsanani da yawa ko da kuwa ya aikata laifin. 

"Mijina ya ce min in yi shiru, ni kuma na ce masa ba zan iya ba tunda babu wani da zai ceci yaron. Na ce kuma bayan komai, ko da ma ya zagi yarinyar, a ina ya koyi hakan, ba a dangin ya koya ba?"

Daga karshe Amina ta bayyana cewa mijin nata ya hasala inda ya ce ya sake ta a kan idon mamaciyar.

"Da na ce zan tafi tunda an sake ni, sai mamaciyar ta durkusa kasa ta fara rokon sa a kan kar ya bari in tafi, saboda za su shiga tashin hankali idan na tafi."

"Washegari bayan na hada kayana sai na ganta a cikin damuwa. Na ce mata idan a kan abin da ya faru ne, kar ta damu saboda a iya sanina komai ya wuce. Cikin rashin sa'a sai ta shiga cikin dakin ta sha maganin kwarin, ta mutu." 

An yi wa Sadiya jana'iza a ranar Litinin kamar yadda Musulunci ya tanadar.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment