Tuesday, 11 June 2019

Sarki Goma: Kalli yanda Dino Melaye ya dauki hankula wajan zaben shuwagabannin majalisa


A wajan zaben 'yan majalisar tarayya da aka yi sanata Dino Melaye ya dauki hankula sosai kama daga lokacin da ya zo wajan saka kuri'a inda sai da ya daga sama sannan ya sakata a akwatin zaben.


Sannan kuma bidiyon Dinon ya bayyana da aka ganshi yana kakkabewa sabon shugaban majalisar kujera wanda abin ya dauki hankula, lura da cewa shi na hannun damar tsohon kakakin majalisar ne, wannan yana nuna cewa yana tafiya da zamani kenan

Kalli bidiyon a kasa:


No comments:

Post a Comment