Monday, 3 June 2019

Sarkin Musulmi Ya Bada Sanarwar Ganin Jinjirin Watan Shawwal

DA DUMIDUMINSA

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III, ya bayar da sanarwar ganin sabon jinjirin watan Shawwal wanda ya kawo karshen azumin watan Ramadan na shekarar 1440 bayan hijra.


Sarkin ya bayyana cewa majalisar ta samu kuri'u ganin watan ne a sassan, Shehun Birni, Machina Yobe, Gwandu da wasu sasssan jihar Sokoto. 

Ya kuma yi kira ga al'ummar Musulmi da su dage da ibadodi da kuma kyawawan abubuwan da suka koya a lokacin azumin watan Ramadan.
Rariya.


No comments:

Post a Comment