Thursday, 6 June 2019

Shekaru Biyar Kenan Da Rasuwar Sarki Kano, Ado Bayero

Ranar 6-6-2014 jihar Kano ta rasa Sarki uba. Arewa ta rasa Sarki shugaba. Nijeriya ta rasa Sarki jagora. 


Rana ce wadda ba zamu taba mantawa da ita a tarihinmu ba. Har gobe muna kewar Dan Abdu. Har gobe ba mu daina kukan mutuwar Dabon Kano ba. Har gobe radadin rashin Dan Bayero yana mana zafi a zuciya.

A yau Dan Abdu Maje Juma'a  yake cika shekara biyar da komawa ga Mahaliccinsa. 

Ni Umar Tofa, ina kara mika sakon gaisuwa ga masoya da al'ummar Kano baki daya bisa rashin gatan makarantun islamiyyu Alh Ado Bayero.

Ina kuma kara mika ta'aziyya ta ga ya'yan Baba.

Allah ya kyautata makwancin Baba. Allah ya sabunta rahma ga Alh Ado Bayero. Allah ya albarkaci bayan Baba. Allah ya kara hada kan ya'yan Baba.

Allah ya kyautata bayansa. 

Allah ya sa Ado Bayero yana aljanna madaukakiya. Amin.
Rariya.


No comments:

Post a Comment