Monday, 17 June 2019

Shugaba Buhari be son daukar hoto>>inji me daukar hoton shugaban kasa


Buhari doesn’t like posing for photos, says presidential photographer
Shahararren me daukar hoton shugaban kasa, Bayo Omoboriowo ya kaddamar da wani littafi me dauke da hotunan yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gudanar da mulkinshi na zangon farko, daga 2015 zuwa 2019.

A hirar da yayi da manema labarai Bayo ya bayyana cewa ya kaddamar da hotunanne dan ya nunawa mutane cewa hoto ba kawai a saka a shafukan sada zumunta bane ko kuma a bango jarida ba, a'a yana dauke da wasu sakonni. kuma yana so idan 'yan baya sun zo su ga yadda mulkin Buhari ya gudana daga 2015 zuwa 2019 sannan kuma yana son ace akwai hotunan na zahiri ba'a shafukan sada zumunta ba kawai yanda idan turawa sun zo zasu ga zahirin Najeriya ba irin wadda ake basu labari ba.

Bayo ya kara da cewa hotunan da yake dauka na shugaban kasar zahirin yanda shugaban yakene babu wata kwaskwarima ko karin gishiri. Yace misali da yawa basu san cewa shugaba Buhari baya son tsayawa dan daukar hoto ba.

No comments:

Post a Comment