Wednesday, 12 June 2019

Super Falcons ta lallasa 'yan matan Koriya ta kudu

Super Falcons na Najeriya sun samu nasarar farko a gasar cin kofin duniya ta mata bayan doke tawagar Koriya ta kudu.


Asisat Oshoala ce ta taimakawa Najeriya doke Koriya ta kudu inda ta jefa kwallo ta biyu, bayan Koriya ta Kudu ta ci kanta ta kafar Kim Do-yeon kafin hutun rabin lokaci.

Najeriya za ta iya zuwa zagaye na biyu idan ta doke Faransa a wasan rukuninsu na karshe a ranar Litinin a Rennes.

Koriya ta kudu kuma za ta kara ne da Norway a ranar Litinin, inda Najeriya za ta yi fatan Koriya ta doke Norway.

A wasan farko, Najeriya ta sha kashi ne hannun Norway ci 3-0.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment