Monday, 24 June 2019

Ta cika mai burinshi bayan da ya bukaci daukar hoto da ita

Wani bawan Allah me suna mubarak Umar ya bayyana irin yanda jarumar fim, Halima ke burgeshi inda ya bukaci daukar hoto da ita a duk sanda ta shirya.Ya aika mata da sakonne ta Twitter bayan da ta saka wasu kyawawan hotunan ta.

Kwana biyu bayan yi maya magana sai gashi sun hadu sun tattauna kuma ta cika mishi burin daukar hoton da ita.

Ya saka hotunan da suka dauka a Twitter inda ya bayyana cewa be yi niyyar saka su ba, ya so ya ajiyene dan tarihi amma tace ya saka dan mutane su shaida.

Ya kara da cewa farin cikin da ya ji ba zai misaltuba.


No comments:

Post a Comment