Saturday, 1 June 2019

Tauraron dan kwallo Reyes ya mutu a hadarin mota

Tauraron dan kwallon kafa Jose Antonio Reyes ya mutu a wani hadarin mota da ya ritsa dashi a Seville kasar Sifaniya yau Asabar. Reyes ya mutu tare da wasu 'yan uwanshi biyu da suke tare a cikin motar.Ya mutu yana da shekaru 35 a Duniya kuma yayi kungiyoyi irinsu Sevilla, Arsenal, Real Madrid da Atletico Madrid.

Wadanda suka yi aiki dashi irin su Arsene Winger, Nwanko Kanu, Thierry Henry, Fabrigas, dadai sauransu sun yi alhinin rashin dan wasan.

Wasu rahotanni sunce a wasan karshe na gasar Champions League da za'a buga yau za'a yi shiru na wasu 'yan mintuna dan nuna Alhini da rashin dan wasan.

No comments:

Post a Comment