Thursday, 13 June 2019

Tsadajjiyar rigar da A'isha Buhari ta saka wajan bikin ranar Dimokradiyya ta jawo cece-kuce

HOTON KAYAN DA AKA CE SUN HAURA NAIRA MILIYAN DAYA DA RABI DA AISHA BUHARI TA SANYA 

A jiya Laraba, 12 ga watan Yuni, 2019 ne uwar gidan shugaban kasar Nijeriya, Hajiya Aisha Buhari, ta sanya wata doguwar bakar riga da 'yan kwakwaf suka ce farashinta ya haura Naira miliyan daya da rabi. Rahotanni sun bayyana cewa tsadar bakar rigar mai suna 'Oscar De Larenta' ya kai Dala 4,290 wanda ya yi daidai da Naira 1,565,850.

DABO FM ta yi rahoton cewa kamfanin da ya dinka kayan, wanda Uwar gidan Shugaban kasa ta sanya yayin halartar walimar bikin ranar dimukuradiyya ta kasa, ya jima da kafuwa a kasar Indiya.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment