Tuesday, 4 June 2019

Virgil Van Dijk ya zama gwarzon dan kwallon mako na Champions League

Tauraron dan kwallon kafar kungiyar Liverpool, Virgil Van Dijk wanda dan wasan bayane kuma shine ya lashe kyautukan gwarzon dan kwallon Premier League na bana da kuna gwarzon dan wasan Ingila na bana saboda gwanin tar da ya nuna.A wasan karshe na gasar cin kofin Champions League da aka buga tsakanin kungiyarshi ta Liverpool da Tottenham shine ya zama gwarzon dan wasan sannan gashi a wannan karin kuma ya zama gwarzon dan wasan Mako na Champions League.
Van Dijk dai yayi bajintar hana kowane dan wasa wuceshi da kwallo a kaf kakar wasan 2018/19 a gasar Premier League da kuma Champions League.

No comments:

Post a Comment